Ma'aikatan mai sun fara yajin aiki a Nigeria

Kungiyar ma'aikatan man fetur da kuma iskar gas na Najeriya, PENGASSAN ta fara wani yajin aiki na sai baba-ta-gani a ranar Alhamis.
A cewar kungiyar, yajin aikin zai dakatar da dukkan wasu ayyuaka a bangaren man fetur da iskar gas na kasar.
PENGASSAN ta fara wannan yajin aiki ne domin matsa wa gwamnati lamba kan wasu bukatu da suka hada da rashin zartar da kudurin dokar yin garanbawul ga bangaren man fetur da kuma korar ma'aikata na bangaren mai.
Ba a dai cimma matsaya ba kan tattaunawar da aka sha yi tsakanin gwamnati da kungiyar.
Wannan yajin aiki dai na iya jefa kasar cikin matsalar karancin mai da kuma jefa tattalin arziki cikin ka-ka-ni-ka-yi.