Bam ya tashi kusa da masallacin Annabi a Madina

Rahotanni daga birnin Madina a kasar Saudiyya na cewa, an kai wani harin kunar bakin wake kusa da masallacin Annabi SAW.
An kai harin ne dai yayin da ake daf da bude baki.
Wani hoton bidiyo ya nuna wata mota da ke cin wuta, wadda ga alama tana ajiye ne a gefen hanya, da kuma jami'an tsaro biyu kwance a gefenta.
Har yanzu dai babu bayanai kan mutuwa ko jikkata.
Masallacin Annabi SAW nan ne kuma inda kabarinsa yake.
Wannan shi ne harin bam na uku da aka samu a kasar Saudiyya a ranar Litinin.
AN kai harin farko ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Jidda, yayin da aka kai hari na biyu wani masallacin Shi'a da ke garin Qatif.

No comments:

Post a Comment