Kwamitin duban wata na fadar mai martaba Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar iii ya ce ba a samu ganin jinjirin watan Shawwal ba a yau 29 ga watan Ramadan.
Wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban kwamitin Farfesa Sambo Wali Junaidu ta ce Sarki Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya ya amince da rahoton kwamitin.
Saboda haka ya yi matsaya cewa watan Ramadan zai cika kwanakki 30 kuma ranar Laraba ita ce ranar daya ga watan shawwal kuma ranar sallah karama.

No comments:
Post a Comment