‘Women In Da’awa’ Ta Kammala Shirin Tallafa Wa Masu Rauni A Neja
Muhammad Awwal Umar
— July 8, 2015 | Leave a comment
Kungiyar mata masu da’awa ta kasa, reshen jihar Neja za ta kashe naira miliyan daya da dubu dari biyar don ciyarwa a cikin wannan wata na Ramadana. Shugabar kungiyar, Amira Rabi’atu Danladi Maku ce ta bayyana haka a lokacin da kungiyar ke rabon kayan abinci ga iyayen marayu da marasa karfi a ofishinsu da ke harabar hukumar kula da harkokin addinin musulunci ta jihar Neja.
Shugabar ta ce a wannan karon rabon kayan abincin bai tsaya kan iyayen marayu kadai ba, aikin rabon ya hada har da masu karamin karfi, wadanda ba sa iya samun abinci a kan lokaci saboda halin rashi. Ta ce, mata masu goyon marayu da ke karkashin kulawar kungiyar, sama da dari ne suka samu rabon farko na tallafin goman farko na Ramadan, yanzu haka kuma suna shirya wasu kayan abincin ga wasu iyayen su kimanin 90, wadanda su ma za su samu a goman tsakiyar Ramadan.
Amira Rabi’atu ta ci gaba da cewa a shekarun baya sun hakkake ne a kan iyayen marayu, sai suka fahimci irin halin da jama’a ke ciki na rashi da kuma rashin samun tallafi, wannan ne ya sa suka fadada aikin nasu don tallafa wa al’umma ta yadda za su samu saukin tafiyar da rayuwar su ta yau da kullun.
Shugabar ta kuma bayyana cewa a wannan wata na Ramadan, kungiyarsu za ta kashe naira miliyan daya da dubu dari biyar kan ciyarwa a lokacin buda baki da kuma sahur a cikin garin Minna. Duk wadannan kudade, in ji ta, suna fitowa ne daga wasu bayin Allah masu kishin taimaka wa al’umma.
“Yanzu haka mun bude sabbin cibiyoyi a wasu Unguwanni da ke cikin garin Minna. A kan haka mun kara yawan jami’an da za su rika kula da yadda aikin zai kasance” in ji ta.
No comments:
Post a Comment