An yanke wa dan Gaddafi hukuncin kisa
Wata kotu a Libya ta yanke hukuncin kisa a kan
dan gidan marigayi Moammar Gaddafi, Saif al Islam da wasu mutane takwas.
Daya daga cikin mutane takwas din da kotun ta yanke wa hukuncin kisa shi ne
Abdallah al-Senousi, tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar.Kotun ta ce ta samu mutanen ne da aikata laifukan yaki a lokacin juyin-juya-halin da ya yi sanadiyar kifar da gwamnatin Moammar Gaddafi a shekarar 2011.
Saif al-Islam dai ba ya kotu a lokacin da aka yanke hukuncin, koda yake ya bayar da shaida ta hanyar bidiyo.
Wasu kungiyoyin masu tayar da kayar baya ne ke ci gaba da tsare shi a garin Zintan.

No comments:
Post a Comment